Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA :Labarin ya kara da cewa hakan ya faru ne tsakanin kauyen ‘Nafi’ah’ da ‘Ainu –Zikri” da suke wajen garin Dar’a a safiyar yau Alhamis.
Kafin haka dai sojojin kasar Siriya sun fara sintiri a wasu yankuna na garin Dar’a bayan ficewar ‘yan ta’adda daga cikinsu, a cikin yan kwanakin da suka gabata.
‘Yan ta’adda wadanda suka yi ta jada baya a fafatawarsu da sojojin gwamnatin kasar a cikin watan da ya gabata, daga karshe sun fice daga wasu yankuna kusa da garin na Dar’a. Amma da alamun sun bibbinne nakiyoyi a wuraren da suka bari don cutar da mutanen yankin ko kuma jami’an tsaron kasar.
Sojojin kasar Siriya basa son yin amfani da karfi wajen fitar da ‘yan ta’adda daga garin Dar’a da gewayenta saboda hakan zai shafi fararen hula da dama, don haka sun fi son a sasanta da su, su fita daga wadannan wurare ciki da fafaren hula kafin su farmasu su kadai.
342/